in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gobara ta lalata sansanin 'yan gudun hijira a arewacin Nijeriya
2019-04-29 09:41:53 cri

Hukumar kula da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA, ta ce akalla matsugunai 140 na 'yan gudun hijira gobara ta lalata a sansaninsu dake jihar Borno na arewa maso gabashin kasar.

Hukumar NEMA, ta ce gobarar da ta tashi ranar Asabar, ta shafi sansanoni biyu na Flatari da Nguro, dake garin Monguno na jihar.

Kakakin hukumar NEMA na shiyyar arewa maso gabas, Abdulkadir Ibrahim, ya shaidawa Xinhua cewa, har yanzu ba a kai ga gano musababbin gobarar ba, amma babu asarar rai.

Akalla matsugunai 28 gobarar ta lalata a sansanin Flatari, yayin da ta lalata 120 a sansanin Nguno, saboda yadda ta yi saurin bazuwa.

Abdulkadir Ibrahim, ya ce akalla mutane 371 gobarar ta raba da matsugunansu, yana mai cewa, an kaddamar da bincike domin gano musababbinta da kuma bukatun wadanda ta shafa.

Ko a ranar 8 ga watan Fabreru, makamancin lamarin da ya auku a garin na Monguno, inda ya yi sanadin mutuwar mutane 3 tare da raba mutane 7,839 da matsugunansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China