in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fashewar bututun mai a kudancin Nijeriya ta yi sanadin mutuwar mutane 19
2018-10-13 15:13:37 cri

Fashewar wani bututun man fetur da sanyin safiyar jiya Juma'a, ta yi sanadin mutuwar mutane a kalla 19 a kauyuka biyu na yankin karamar hukumar Osisioma, na jihar Abia dake kudancin Nijeriya.

Shugaban rundunar tsaro da wanzar da zaman lafiya ta Civil Defense a jihar Benito Eze ne ya tabbatar da adadin wadanda lamarin ya rutsa da su ga kafafen yada labarai a Umuahia, babban birnin jihar.

Benito Eze ya ce, mutane 16 ciki har da mace guda ne hatsarin ya rutsa da su a kauyen Umuaduru, inda wasu matasa a yankin ke dibar man fetur daga bututun da aka lalata.

A cewar shugaban rundunar ta Civil Defense, wasu mutane 3 kuma sun mutu sanadiyyar gobarar da ta tashi a wani gida dake yankin kauyen Umuimo.

Tuni rundunar ta aike da jami'anta don killace wurin don kare karuwar hatsarin. Daga bisani dai jami'an kwana-kwana sun yi nasarar kashe gobarar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China