in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya na dakon sakamakon gwajin riga kafin cutar malaria na farko
2019-04-27 15:15:59 cri

Gwamnatin Nijeriya ta ce, tana dakon sakamakon gwajin riga kafin cutar malaria na farko a duniya, wanda aka yi gwajinsa kwanan nan a kasar Malawi.

Ministan lafiya na kasar Isaac Adewole, ya shaidawa manema labarai jiya a birnin Abuja cewa, idan riga kafin ya yi aiki yadda ya kamata, zai taimakawa Nijeriya da ma duniya baki daya wajen yaki da cutar malaria.

Isaac Adewole ya ce, Nijeriya ce ke da kaso 25 cikin dari na matsalar cutar a duniya, sannan ita ta dauki kaso 19 na jimilar mace-macen da cutar ke haifarwa a duniya, yana mai cewa, sakamakon riga kafin zai inganta kokarin kasashen duniya na kawar da malaria.

Duk da ana jiran sakamakon gwajin, kasar na kara jajircewa da taimakon wasu hukumomi abokan hulda wajen fatattakar cutar.

Akalla 'yan Nijeriya miliyan 53.7 ne ke kamuwa da cutar malaria, sannan 81,640 daga cikinsu ne ke mutuwa a duk shekara.

Har ila yau, kasar ce ke da kaso 53 cikin dari na masu kamuwa da cutar a yankin yammacin Afrika.

Ministan ya ce, Nijeriya ta kuduri niyyar kawar da cutar. Yana mai cewa, sun kirkiro shirye-shiryen da za su inganta samun kudaden aiwatar da shirye shiryen yaki da cutar malaria. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China