in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan bindiga sun kashe mutane 2 a arewacin Nijeriya
2019-04-21 15:55:59 cri

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kai hari wani wurin shakatawa a jihar Kaduna dake arewacin Nijeriya da sanyan safiyar jiya Asabar, inda suka kashe masu yawon bude ido 2, ciki har da mace guda.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce, 'yan bindigar dauke da muggan makamai sun kuma sace wasu masu yawon bude ido 3.

Kakakin rundunar Yakubu Sabo ne ya tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jihar.

Yakubu Sabo, ya ce wasu 'yan bindiga sun yi wa wajen shakatawa da ake kira da Kajuru Castle tsinke, inda suka bude wuta kan masu yawon bude ido, tare da kashe mutane biyu nan take.

Jami'in ya ce, jami'an sintiri sun kwashe mutanen da suka mutu, wadanda aka yi ammana sun je yawon bude ido ne daga birnin Lagos, cibiyar hada hadar kasuwanci ta kasar, inda aka garzaya da su asibitin St. Gerard dake kwaryar birnin Kaduna. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China