Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya ce damuwarsa na karuwa game da yawan take hakkokin yara a Mali, kamar kisan yara 46 a ranar 23 ga watan Maris a garin Bankass, tare kuma da rufe makarantu.
Kakakin UNICEF Christophe Boulierac ya bayyanawa MDD a Geneva cewa, tabarbarewar yanayin jin kai a Mopti dake yankin tsakiyar Mali saboda rikicin kabilanci da kasancewar kungiyoyi masu dauke da makamai na kara shafar yara masu rauni.
Ya ce, kusa 1 bisa 3n dukkan makarantun yankin Mopti a rufe suke yanzu saboda rashin tsaro, al'amarin dake barazana ga hakkin ilimin yara sama da 157,000 daga cikin yara 260,000 da rufe makarantu a kasar ya shafa.
UNICEF na aiki kafada da kafada da jami'an ba da ilimi a yankunan dake fama da rikici da ma'aikatar ilimi ta kasar, da nufin samar da ilimi mai dorewa ga wadancan yara ta hanyoyin dabaru na wuci gadi kamar koyarwa a cibiyoyin koyo na unguwanni. (Fa'iza Msutapha)