in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF ya bukaci a kawo karshen take hakkokin yara a yankunan dake fama da rikici
2017-12-29 09:34:57 cri

Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF ya yi kira ga bangarorin dake rikici su kiyaye dokokin da ke kare hakkokin yara, tare da kawo karshen take hakkokinsu da hare-haren da ake kai musu ba tare da bata lokaci ba.

Cikin wata sanarwa da asusun ya fitar, daraktan sashen ba da agajin gaggawa na asusun Manuel Fontaine, ya ce yara na fuskantar hare-hare a gidajensu da makarantu da wuraren wasa.

Ya ce, yayin da ake ci gaba da fama da rikice-rikice, ba za su yi shiru game da batun ba. Yana mai cewa, ba zai yuwu a saba da irin wannan aika-aika ba.

A cewar UNICEF, yara su ne suka fi fuskantar hare-hare, domin ana amfani da su a matsayin kariya, sannan kuma ana kashe su tare da horar da su tare da amfani da su yayin fadace-fadace a duniya.

Har ila yau, asusun ya ce, cin zarafi ta hanyar lalata da auren dole da satar mutane sun zama abubuwan da ake yi a wuraren da ake rikici da suka hada da Iraqi da Syria da Yemen da Nijeriya da Sudan ta Kudu da kuma Myanmar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China