in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF ta yi kashedin karancin abinci mai gina jiki a yankin arewa maso gabashin Najeriya
2016-12-14 09:41:54 cri

Babban daraktan asusun yara na MDD UNICEF Anthony Lake, ya yi kashedi game da kamfar abinci mai gina jiki da ake fuskanta a yankunan arewa maso gabashin Najeriya, sakamakon tashe tashen hankula masu alaka da rikicin Boko Haram.

Cikin wata sanarwa da ofishin sa ya fitar, Mr. Lake ya ce, jihohin da wannan matsala ta fi kamari sun hada da Borno, da Yobe da kuma Adamawa. Hakan kuwa na da nasaba da yadda wancan rikici ya janyo dakatar da harkokin noma da kiwo a gonaki masu yawa dake wadannan jihohi. Ya ce, ko shakka babu wannan matsala ta yi matukar tasiri ga rayukan kananan yara.

Jami'in ya kara da cewa, akwai mutane da yawan su ya kai miliyan 4 da dubu dari 6 dake fama da yunwa a wannan yanki, ciki hadda kimanin mutane miliyan 2 dake bukatar tallafin gaggawa.

Asusun UNICEF dai ya ce, nan da shekara mai zuwa, kimanin yara 400,000 ne za su iya fuskantar mawuyacin hali na karancin abinci mai gina jiki a jihohin 3, kana akwai yiwuwar rasuwar yaro daya cikin ko wane yaro 5, muddin ba a kai dauki na kula da lafiya a jihohin ba.

Yankin arewa maso gabashin Najeriya dai ya kasance tungar kungiyar Boko Haram, ko da yake cikin watannin baya bayan nan gwamnatin kasar na daukar karin matakan soja a yankin, a wani mataki na kawo karshen ayyukan tada kayar baya daga mayakan kungiyar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China