in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#BRF2019# Xi Jinping: Bangaren Sin zai kulla yarjejeniyoyin bunkasa cinikayya ba tare da shinge ba da karin kasashe
2019-04-26 11:15:45 cri
A yau Juma'a, a yayin bikin kaddamar da taron kolin hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu ko kuma BRF a takaice a Beijing, shugaban kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kulla yarjejeniyoyin bunkasa cinikayya ba tare da shinge ba bisa sabbin ma'auni mai inganci da karin kasashe da yankuna, sannan za su kara yin hadin gwiwa a fannonin kwastam da haraji da kuma harkokin safiyo, kuma za a bullo da wani tsarin yin hadin gwiwa a fannin biyan haraji kan kayayyakin dake shafar shawarar "ziri daya da hanya daya". A waje daya kuma, za su yi hadin gwiwa a fannin amincewa da juna kan takardun shaida na "ba da izinin yin kasuwanci", bugu da kari, za a yi kokarin bunkasa shawarar "ziri daya da hanya daya" ta hanyar musayar muhimman bayanai, ta yadda za a kirkiro sabbin hanyoyin bunkasa shawarar.

Xi Jinping ya kuma kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da shirin kirkiro sabbin fasahahoin zamani a lokacin da ake aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", wato a cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta tallafa wa mutane dubu 5 na gida da na waje wadanda suke kirkiro sabbin fasahohin zamani ta yadda za su yi mu'amala da samun horo da kuma yin nazari cikin hadin gwiwa. Dadin dadawa, kasar Sin za ta nuna goyon baya ga masana'antun kasashe da yankuna daban daban kan yadda za su yi hadin gwiwa wajen samar da kayayyakin sadarwa na more rayuwar al'umma, ta yadda za a iya daga matsayin yanar gizo ta sadarwa a tsakaninsu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China