A jawabin da ya gabatar, shugaban ya ce, tun lokacin da kasashen biyu suka fara hadin gwiwa da juna a fannin harkokin diplomasiyya, kawo yanzu hadin gwiwarsu ta kai wani babban matsayi. Ya ce, kasashen biyu sun aiwatar da hadin gwiwar samun moriyar juna bisa la'akari da moriyar kasashen biyu. Sabo da haka, shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar ta dace da moriyar kasar Sin, da ta kasar ta Djibouti.
Shugaban ya kara da cewa, kasar Djibouti na da damar samun babban kason cinikin teku da ake gudanarwa bisa la'akari da yankin da take, kuma za ta yi amfani da wannan dama, ta samar da yanayin ciniki mai inganci. Ya kara da cewa, kasarsa na matukar bukatar jari a fannonin harkokin yawon shakatawa da makamashi da kuma manyan ayyuka, kuma tana fatan amfana da wannan dama.(Lubabatu)