in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Putin ya ce hanyar lumana ce kadai za ta kai ga warware matsalar nukiliya a zirin koriya
2019-04-25 20:53:32 cri

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya ce ta aiwatar da matakan lumana ne kadai za a iya kaiwa ga warware matsalar nukiliya da ake fuskanta a zirin koriya. Shugaba Putin ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, yayin wata liyafa da aka shirya, domin maraba da jagoran kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un wanda ke ziyara a Rasha.

Ya ce a nata bangare Rasha, a shirye take ta yi hadin gwiwa da sauran sassa, wajen tabbatar da an kai zuciya nesa a zirin na koriya, za kuma ta taimaka wajen karfafa tsaro a yankunan arewa maso gabashin Asiya baki daya.

Putin ya kuma ce yana da tabbacin cewa, muddin kasashen duniya masu alaka da wannan batu, da ma sauran sassan masu ruwa da tsaki suka yi hadin kai, to ko shakka babu za a kai ga cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da lumana, da wadata mai dorewa a zirin koriya.

Kafin liyafar, wakilan Rasha da na Koriya ta arewa, sun zanta da juna, kana kuma shugabannin kasashen biyu suka gana da juna kai tsaye.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China