Kafin hakan, fadar shugaban kasar Amurka wato White House ta sanar da cewa, shugaba Trump da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un za su yi gajeren tattaunawa yau da dare, daga baya su ci abinci tare, sannan kuma su yi shawarwari a gobe 28 ga wata. A yinin yau kuma, shugaba Trump zai tattauna da shugabannin kasar Vietnam.
Kafin shugaba Trump ya tashi zuwa birnin Hanoi, ya bayyana cewa yana fatan za a cimma sakamako kan wannan shawarwari.
A watan Yunin shekarar 2018, Trump da Kim Jong-un sun yi ganawa ta farko a kasar Singapore tare da daddale hadaddiyar sanarwa, inda suka cimma daidaito kan kafa sabuwar dangantaka tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa da kuma tsarin kiyaye zaman lafiya mai dorewa a zirin Koriya. (Zainab)