in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar MDD ta bayyana rawar da shawarar ziri daya da hanya daya za ta taka wajen gina Afrika
2019-04-11 14:54:36 cri

Vera Songwe, babbar jami'ar hukumar tattalin arziki ta MDD mai kula da nahiyar Afrika (UNECA), ta yabawa shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar bisa irin rawar da za ta taka wajen shawo kan matsalolin da suka shafi fannin samar da ababen more rayuwa da guraben ayyukan yi.

Songwe ta fadawa kamfanin dillancin labaran Xinhua na kasar Sin cewa, shawarar ziri daya da hanya daya ta haifar da kyakkyawan tasiri wajen kyautata rayuwar miliyoyin jama'ar kasashen Afrika daban daban, kana za ta taimakawa kasashen Afrikan wajen bunkasuwar kayayyakin more rayuwa wadanda al'ummar nahiyar ke matukar bukatar su.

A shekarar 2013 ne kasar Sin ta gabatar da shawarar da nufin hadin gwiwar kasa da kasa don bunkasa ci gaba tare da nufin cin moriya tare, shawarar ziri daya da hanya daya ta shafi batun hadin gwiwar gina muhimman kayayyakin more rayuwa, da mu'amalar ciniki da zuba jari, da kuma kyautata huldar dake tsakanin mutum da mutum da nufin samar da ingantaccen ci gaban rayuwar bil adama a fadin nahiyoyin duniya.

"Shawarar ziri daya da hanya daya wata kila ita ce shawara mafi girma da za ta bunkasa ci gaban duniya baki daya," in ji jami'ar MDDr.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China