in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNEP na goyon bayan aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" ba tare da gurbata muhalli ba
2019-04-25 14:06:18 cri


Daga yau zuwa Asaba mai zuwa ana gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa dangane da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" karo na 2 a birnin Beijing na kasar Sin. Jorce Msuya, mukaddshiyar darektar zartaswa ta hukumar kula da muhalli ta MDD wato UNEP, ta zanta da wakiliyarmu kafin ta tashi zuwa Beijing domin halartar taron. Inda Madam Msuya ta ce, shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" tana taimakawa wajen kara azama kan cimma manufar MDD ta samun ci gaba mai dorewa. Hukumar UNEP kuma za ta goyi bayan aiwatar da shawarar ba tare da gurbata muhalli ba, tare da mara wa kasar Sin baya wajen yin musayar kyawawan fasahohinta ta fuskar kiyaye muhalli da kasashe masu alaka da shawarar.

A matsayinta na jagora da kuma wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen kula da harkokin muhalli karkashin inuwar MDD, hukumar UNEP ta nuna babban goyon baya kan shawarar da kasar Sin ta gabatar ta "Ziri Daya da Hanya Daya". Madam Msuya tana da nata ra'ayi dangane da shawarar, inda ta ce, "Ruhun shawarar 'Ziri Daya da Hanya Daya' da kuma manufarta su ne zuba jari kan manyan ababen more rayuwar jama'a, lamarin da ya kara azama kan aiwatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030. Ganin haka ya sa na yi farin ciki sosai. Ina kuma fatan kara fahimtar shawarar a yayin taron, tare da kulla hulda da kasashe masu ruwa da tsaki. A matsayinta na mambar MDD, hukumar UNEP za ta ci gaba da aiwatar da manufar samun ci gaba mai dorewa."

A yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa dangane da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" karo na 1 da aka yi a shekarar 2017, an gabatar da burin kafa kawancen duniya na aiwatar da shawarar ba tare da gurbata muhalli ba. Yanzu hukumomi fiye da 80 sun kulla kawance, wanda shi ma ya samu goyon baya daga hukumar UNEP. Madam Msuya ta ce, galibin jarin da za a zuba kan manyan ababen more rayuwar jama'a za su yi tasiri ga muhalli, ko mai kyau ne, ko kuma maras kyau. Don haka hukumar ta UNEP za ta bai wa sassa daban daban masu ruwa da tsaki shawara, dangane da barazana ga muhalli. Madam Msuya ta ce, "Babban aikinmu shi ne hada kai da kasashen da ke cikin 'Ziri Daya da Hanya Daya' bisa tsarin shawarar, na kara fahimtar barazanar da kila za su fuskanta ta fuskar kiyaye muhalli, da kuma yadda za mu goyi bayan wadannan kasashe don su kyautata karfinsu ta hanyar ba su shawara. Kana kuma, a matsayinta na hukumar MDD, UNEP na ba da gudummowa wajen samun ci gaba mai dorewa. Za mu mai da hankali kan kasashen da suka halarci shawarar 'Ziri Daya da Hanya Daya', inda za mu kalli yadda aka samar da guraben aikin yi bisa jarin da aka zuba musu, da kuma tabbatar da zuba dauwamammen jari kan aikin gona da makamashi ba tare da gurbata muhalli ba."

Madam Msuya ta dauki shekaru da dama tana zaune a kasar Sin. Saboda haka ta fahimci kyautatuwar yanayin kasar Sin da kanta. Ta yi nuni da cewa, yadda kasar Sin ta daidaita gurbatar iska, ya zama wani misali mai kyau kuma abin koyi. Kasar Sin tana yayata ra'ayin kiyaye muhalli, tare da daukar matakan da suka dace, a kokarin ganin gwamnati da al'umma su shiga aikin kiyaye muhalli. Sa'an nan kuma kasar Sin ta taimaka wa wasu masana'antun samar da manyan injuna su canza salonsu, ta yadda za su fara amfani da makamashi mai tsabta. A ganin Madam Msuya, kyawawan fasahohin da kasar Sin ta samu sun cancanci musaya da sauran kasashe masu tasowa. Madam Msuya ta ce, "Wasu kasashen da suka halarci shawarar 'Ziri Daya da Hanya Daya' da kasashe masu tasowa suna neman yin koyi da kasar Sin. Yaki da gurbatar iska, wani misali ne mai kyau. Amma ba shi kadai ba ne. Kasar Sin tana iya gabatar da wasu kyawawan fasahohinta a kan batutuwan tsaftace ruwa, makamashi, gandun daji, raya birane da dai sauransu."

Madam Msuya ta kuma ba da shawarar cewa, nan gaba za a goyi bayan sabbin hanyoyin tattara kudi da ba sa gurbata muhalli, da kuma barin makamashin da ake sake sabuntawa ya taka rawa wajen raya manyan ababen more rayuwar jama'a. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China