in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO:An kaddamar da alluran riga kafin zabbabin cizon sauro na farko a Malawi
2019-04-24 10:24:11 cri
Babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Dr. Tedros Adhanom Grebreyesus ya sanar da cewa, an kaddamar da alluran rigakafin zazzabin cizon sauro irinsa na farko jiya Talata a kasar Malawi, a wani mataki na gwada shirin da ake fatan zai kare, musamman dubban daruruwan yara 'yan kasa da shekaru biyar, daya daga cikin cututtukan dake kisa a duniya.

A cewar hukumar ta WHO, a cikin shekaru 30 da suka gabata, nauyin allurar RTS,S shi ne na farko kuma rigakafi da ake ganin zai rage zazzabin na cizon sauro tsakanin yara. Gwaje-gwajen da aka yi, sun nuna cewa, alluran riga kafin za ta iya kare kimanin 4 cikin 10 na cutar ta maleriya, ciki har da uku cikin goma na matsananciyar cutar ta maleriya dake iya kisa.

Grebreyesus ya ce, alluran riga kafin, tana iya zama wata sabuwar silar ceton dubbban rayukan kananan yara a duniya.

Kasar Malawi, ita ce ta farko cikin kasashen Afirka uku da za a samar da alluran rigakafin ta RTS,S ga yara masu shekaru biyu, yayin da za a kaddamar da alluran rigakafin a kasashen Ghana da Kenya cikin makonni masu zuwa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China