in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar WHO ta yi kira ga bada hidimar magance cutar daji
2018-02-04 13:36:23 cri
Yau ranar 4 ga watan Febrairu rana ce ta yaki da cutar daji ta duniya. Hukumar lafiya ta duniya WHO, da abokan aiki na yaki da cutar daji na duniya sun yi kira a kwanakin baya da a samar da hidimar bincike da bada jinya ga cutar daji ga dukkan mutanen duniya da matakai na daidaiku. Hukumar WHO ta yi nuni da cewa, ana iya magance cutar daji da a kalla kashi daya cikin kashi uku a duniya.

Taken ranar yaki da cutar daji ta duniya na bana shi ne "Mun iya, Na iya", a hakika shi ne wani shiri na tsawon shekaru 3 wato daga shekarar 2016 zuwa 2018, an yi kira ga kowane mutum da ya samar da gudummawa wajen yaki da cutar daji don rage yawan mutanen da suka kamu da cutar a duniya.

Kawancen yaki da cutar daji na duniya ya gabatar da sanarwa a kwanakin baya cewa, yana fatan yin amfani da damar ranar yaki da cutar daji ta duniya wajen sa kaimi ga mutane da su yi bincike da samun jinya kan cutar daji a matakai na daidaiku, ta haka za a iya ceto karin rayukan mutane a duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China