in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rashin isassun kudi ka janyo jinkiri wajen tunkarar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
2019-02-27 10:23:33 cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi gargadin cewa, shawo kan cutar Ebola dake ci gaba da bazuwa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, kai ya fuskantar hadarin jinkirin saboda rashin isassun kudi.

Darakta Janar na hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesusu, ya yi kira ga masu bada gudunmawa da su ci gaba da bada kudi domin shawo kan bazuwar cutar a kasar, ko kuma a samu komawa baya. A cewarsa, daga cikin dala miliyan 148 da abokan hulda masu aikin shawo kan cutar ke bukata cikin gaggawa domin ci gaba da gudanar da aikinsu, dala miliyan 10 kawai aka samu kawo yanzu.

A cewar wata sabuwar kididdiga da hukumar ta fitar, sama da mutane 80,000 a Jamhuriyar Demokadiyyar Congo ne aka yi wa rigakafi, sannan sama da mutane 400 sun samu kulawar lafiya. Har ila yau, an gano sama da mutane 40,000 da suka yi mu'amala da masu cutar, wadanda a kullum ake duba su tsawon makonni 3, domin tabbatar da su ma ba su kamu da rashin lafiya ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China