Wata sanarwar da WHO din ta fitar, ta ce an samu nasarar takaita yaduwar cutar zuwa sabbin wurare, kuma yanayin na daidatuwa a cibiyar lafiya ta Mabalako dake Mangina na lardin arewacin Kivu, inda kuma a yanzu ayarin jami'an lafiya ke ci gaba da inganta ayyukan takaita cutar a Beni da Butembo, wadanda su ne manyan birane biyu a lardin, domin kare yaduwar cutar zuwa sauran yankuna.
Har ila yau, WHO ta yi gargadin cewa, har yanzu akwai barazanar ci gaba da yaduwar cutar, inda ta ce kalubalen dake akwai su ne na rashin gano wadanda suka yi mu'amala da masu cutar da jinkirin gano cutar a cibiyoyin lafiya da rashin kyawawan matakan kariya da rashin amincewar wasu masu dauke da cutar na zuwa asibitocin da aka ware domin su.
Ta kara da cewa, har yanzu abun da aka mayar da hankali kai shi ne karfafa duk cibiyoyin kiwon lafiya don tunkarar cutar a dukkan yankuna da kuma ci gaba da inganta zama cikin shiri da tunkarar cutar a larduna da kasashe makwabta da babu cutar. (Fa'iza Mustapha)