in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar sojan Sudan ta yi alkawarin mika mulki ga farar hula
2019-04-22 10:27:48 cri
Shugaban majalisar sojoji ta wucin gadi dake kasar Sudan, Abdel-Fattah Al-Burhan, ya bayyana kudurin majalisar na mika mulki ga farar hula.

Al-Burhan wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da gidan talabijin na kasar, ya ce, aikin majalisar shi ne taimakawa masu zangar-zangar, su kuma mika mulki ga farar hula kamar yadda masu zanga-zangar juyin-juya halin suka bukata.

Ya ce, majalisar ba ta da niyyar zama a kan karagar mulki, kuma nan ba da dadewa ba za su fara shirye-shiryen mika mulki.

Ya kara da cewa, yanzu haka, majalisar ta karbi sama da matakan warware takaddamar siyasar kasar guda 100 daga bangarorin siyasar kasar daban-daban. Shugaban ya kuma lashi takwabin cewa, babu wani bangare na siyasar kasar, in ban da tsohuwar jam'iyyar NCP da ta jagoranci kasar da ba za a sanya ta cikin shirin mika mulkin ba.

Ya kuma bayyana cewa, an samu tsabar kudi euro miliyan 7 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 7.87 da dalar Amurka 350000 da biliyoyin fama-faman kudin kasar a gidan tsohon shugaban kasar da aka hambarar Omar al-Bashir.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China