Wata sanarwa da kwamitin siyasa na majalissar ya fitar a ranar Alhamis, ta ce aikin majalissar shi ne jagorantar kasar kafin lokacin da za a kafa zababbiyar gwamnati.
An fitar da sanarwar ne dai, bayan kammala zaman tattaunawa tsakanin sashen siyasa da na sojin kasar da wakilan kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa dake ayyukan su a cikin kasar.
Yayin zaman an gudanar da shawarwari da suka jibanci batun tsaro, da na siyasa, da ma batun kafa gwamnatin farar hula, da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin siyasar kasar.
Tuni dai majalissar ta soji karkashin jagorancin shugaban ta Abdel-Fattah Al-Burhan, ta fara daukar wasu matakai masu nasaba da bukatun masu zanga zangar a sassan kasar ta Sudan. (Saminu Alhassan)