in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana bukatar jam'iyyun Sudan su cimma daidaito a lokacin mulkin wucin gadi
2019-04-21 17:24:26 cri
Wata sanarwa da kwamitin mulkin soja na wucin gadi na kasar Sudan ya fitar a jiya, ta ce shugaban hukumar kungiyar AU Moussa Faki ya bayyana a wannan rana cewa, ana bukatar jam'iyyun Sudan su cimma daidaito a lokacin mulkin wucin gadi.

Sanarwar ta bayyana cewa, shugaban kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin mulkin soja na wucin gadi na kasar Sudan Omar Zain al-Abideen ya tattauna da Mr Faki a fadar shugaban kasar a wannan rana, inda suka tattauna yadda kungiyar AU za ta samar da goyon baya ga Sudan don daidaita matsaloli a lokacin mulkin wucin gadi na yanzu.

Mr Faki ya bayyana cewa, Sudan muhimminyar kasa ce a nahiyar Afirka, kuma abu mafi muhimmanci shi ne rage bambance bambance da cimma daidaito da juna, kana ana bukatar jam'iyyun kasar su cimma ra'ayi daya a lokacin mulkin wucin gadi na yanzu.

Sanarwar ta kara da cewa, kwamitin mulkin soja na wucin gadi na kasar yana kokarin samar da yanayi mai kyau ga bangarorin siyasa su kama mulki cikin lumana. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China