in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane uku sun mutu a harin 'yan bindiga a arewacin Najeriya
2018-10-18 09:23:32 cri

Hukumar 'yan sanda a Najeriya ta tabbatar da cewa an hallaka jami'anta biyu da wani direba farar hula guda a wani harin da 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba suka kaddamar da safiyar ranar Laraba a jahar Kaduna dake arewacin kasar.

Yakubu Sabo, kakakin hukumar 'yan sandan, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an raunata wasu 'yan sandan guda 5 a lokacin harin, kuma ana ba su kulawa a asibitin jihar.

Jami'an 'yan sandan sun fita aikin sintiri ne a yankin Kakuri dake jihar Kaduna, kafin daga bisani 'yan bindigar suka afka musu.

Sabo ya ce, an yi musayar wuta a lokacin kai harin, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an 'yan sandan biyu. Wani direba farar hula dake wucewa ta inda lamarin ya auku ya gamu da ajalinsa bayan da harsashin da 'yan bindigar suka harba ya fada masa, inda ya mutu a wani asibitin dake yankin, hakan ya kawo adadin wadanda suka mutun ya kai mutane uku.

Kakakin 'yan sandan ya ce, babu wani makami da maharan suka yi awon gaba da shi saboda karfin bindigar da 'yan sandan ke amfani da ita.

A cewarsa, maharan sun tsere da raunuka a jikinsu, ya kara da cewa, sai dai tuni an baza jami'ai domin zakule su don gurfanar da su a gaban shari'a.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China