in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan bindiga sun hallaka mutane 6 a arewa maso yammacin Najeriya
2018-10-28 15:05:59 cri

Wasu 'yan bindiga wadanda ba'a san ko su wane ne ba sun hallaka akalla mutane 6, ciki har da wani jami'in 'dan sanda mai mukumin kofural, a jihar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda hukumar 'yan sandan yankin ta sanar da hakan a jiya Asabar.

An kuma jikkata wasu mutane 3 bayan da maharan suka afkawa kauyen Gurbin Bore, dake yankin karamar hukumar Zurmi, da yammacin ranar Juma'a. Kimanin maharan 100 ne suka yiwa kauyen tsinke.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Zamfara Mohammed Shehu, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, maharan sun cinnawa wasu motoci 11 wuta, ciki har da wata motar 'yan sanda. Haka zalika sun kone wasu babura 3 na mazauna kauyen.

Shehu yace ana cigaba da bincike domin zakulo maharan.

Ya ce, 'yan sanda suna zargin maharan sun fito ne daga dajin Dumburum, wajen da aka yi amanna maharan sun mayar da shi a matsayin sansaninsu.

Wani jami'in gwamnati a yankin ya fadawa 'yan jaridu cewa, maharan sun kone wasu shaguna 13.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China