in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikici a jihar Taraban Nijeriya ya yi sanadin mutuwar mutane 73
2018-07-14 15:37:46 cri

Rikicin kabilanci a jihar Taraba dake arewa maso gabashin Nijeriya, ya yi sanadin mutuwar mutane 73.

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta kasar, Sahabi Mahmoud, ya shaidawa manema labarai a Jalingo, babban birnin jihar cewa, rikicin da aka fara tun ranar 5 ga wata, ya yi sanadin mutuwar mambobin kungiyarsa 23.

Ya ce an tabbatar da mutuwar mutane 73, sannan an kone kauyuka kusa 50, sanadiyyar sabon rikicin da ya barke tsakanin kabilun Hausa-Fulani da na Yandang dake yankin Lau na jihar.

Ya kara da cewa, sama da 'yan kabilar Hausa-Fulani 3,000 ne suka rasa matsugunansu, kuma galibin mata da yara da suka tsere na samun mafaka a sakatariyar kungiyar Musulmi dake birnin Jalingo, yayin da wasu ke yankunan kananan hukumomin dake makwabtaka da yankin.

A nasa bangaren, wani dattijon kabilar Yandang, Aaron Artimas, ya ce sama da mutane 50 'yan kabilarsa da sauran wasu kabilu na yankin ne aka tabbatar da mutuwarsu sanadiyyar rikicin.

Aaron Artimas, ya kuma dora alhakin sake barkewar rikicin a kan wasu mutane dake wajen yankin, wadanda ke ingiza rikicin domin cimma moriyarsu ta kashin kai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China