Kamfanin kera jiragen kasa na CRRC na birnin Changchun ya samar da jiragen kasa na zamani ga kasar Isra'ila



A kwanakin baya, kamfanin kera jiragen kasa na CRRC na birnin Changhun na kasar Sin ya samar da jiragen kasa na zamani ga kasar Isra'ila domin amfani da su a hanyoyin jiragen kasa na zamani da ake gudanar a kasar, wannan ne karo na farko da Sin ta fitar da irin wadannan jiragen kasa na zamani ga kasar mai ci gaba, kana irin jiragen kasan sun zama a matsayin gaba a fannin tabbatar da tsaro a duniya.
A halin yanzu, kamfanin CRRC na birnin Changchun na kasar Sin ya riga ya fitar da kayayyakinsa zuwa kasashe da yankuna fiye da 20 ciki har da Australia, da Amurka, da Singapore, da Thailand, da Habasha da sauransu, yawan jiragen kasa da aka samar ya kai fiye da 8900. (Zainab)