Za dai a kawo karshen gwajin ne a karshen watan Satumba, zai kuma samar da tallafin fasaha ga aikin gina hanyoyin dogo mai saurin gaske, wadanda za su hada biranen Beijing da Zhangjiakou da kuma biranen Beijing da Xiongan. An ce, gwajin da ake gudanarwa a wannan karo zai shafi wasu fannoni 27, ciki har da tsarin samar da wuta.
Kasar Sin na sa ran hada sabbin fasahohin sadarwa da kuma fasahohin harhada jiragen kasa masu saurin gaske, don neman kyautata fasahohin zamanin da ake amfani da su a fannonin harhada jiragen kasa masu saurin gaske, da kuma tafiyar da su, ta yadda za a kara inganci da kiyaye muhalli da kuma dadi ga jiragen. (Lubabatu)