in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar sufurin jiragen kasa ta Sin tana shirin yin jigilar masu bulaguro a lokacin zafi
2017-06-15 10:08:41 cri

Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta kasar Sin ta fara shirin yin jigilar fasinjoji kimanin miliyan 598 wadanda ake sa ran za su yi zirga zirga a lokacin hutun lokacin zafi.

Bisa ga adadin matafiyan, ana sa ran mutane sama da miliyan 9 da dubu 650 ne za su yi jirga jirga a ko wace rana, wanda ake sa ran farawa tsakanin ranar 1 ga watan Yuli zuwa 31 ga watan Agusta, kamar yadda hukumar zirga zirgar jiragen ta kasar CRC ta bayyana.

An samu karin kashi 9.1 cikin 100 idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.

Kasancewa a wata mai zuwa za'a fara zirga zirgar, hukumar kula da sufurin jiragen kasan za ta kara yawan jirage 46 domin su wadaci adadin fasinjojin da ake sa ran karuwarsu.

Kasar Sin tana da ingantaccen tsarin sufurin jiragen kasa. Ya zuwa karshen shekarar 2016, Sin tana da adadin kilomita dubu 124 da ya hade sassan kasar, hakan ya ba ta damar zama kasa mafi girma a duniya da ta mallaki jirage masu saurin tafiya da ya zarta kilomita dubu 22.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China