Wata sanarwa da aka fitar, ta ruwaito manajan hukumar kula da baje kolin Koecler Jochen, wanda ya bayyana haka a jiya na cewa, jimilar masu baje koli 6,500 daga kasashe da yankuna 75, ciki har da hukumomin kasa da kasa da kanana da matsakaitan kamfanoni ne suka hallara domin taron na bana.
Ya ce masu baje koli Sinawa 1,300 ne suka hallara, inda ya ce kasar Sin yanzu na bada gudunmuwa ga kirkire-kirkire, yayin da kuma take lalubo hanyoyin kirkire kirkire a sabon zamanin da ayyukan masana'antu ke ciki na Industry 4.0, wanda shi ma yake mayar da hankali kan fasahar AI da makomar ayyukan masana'antu.
Koeckler Jochen ya kara da cewa, a daya bangaren kuma, kasar Sin muhimmiyar kasuwa ce ga fasahar masana'atu, kuma tuni kasar ta mallaki fasahohin da kayayyakin masana'antu na zamani. (Fa'iza Mustapha)