A watan Aflilun bara ne, aka fara aikin gyara kebabben yankunan masana'antu dake wajen yankin Shunde na birnin Foshan na lardin Guangdong ne, domin kara farfado da kauyuka, da amfani da filayen kasa yadda ya kamata, da kuma inganta tsarin masana'atu. A bara gwamnati ta samar da kudin RMB biliyan 2.266, da jawo jarin al'umma kimanin biliyan 5.563 don gyara kebabben yankunan masana'antu.
Bayanai na cewa, kebabben yankin masana'antun Baoyong na kauyen Xiantang yana da fadin muraba'in mita 153.72, inda ake shirin kafa wata ma'aikata mai fadin muraba'in mita dubu 270. Ana saran wannan aikin zai gyara da kafa ma'aikatu na zamani, da jawo kamfanoni masu inganci da dabarun gudanarwa masu kyau, da jawo sana'ar gina gidaje ta zamani, da kyautata sana'ar kayan gida ta gargajiya, don kara inganta masana'antun wurin a dukkan fannoni. (Bilkisu)