in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta ce raya ababen more rayuwa na da muhimmanci ga ci gaban Afrika
2019-04-17 10:36:24 cri

Wakilin AU kan ayyukan raya ababen more rayuwa Raila Odinga, ya ce kasashen Afrika na bukatar ware kudi ga ayyukan raya ababen more rayuwa domin samun ci gaba.

Yayin wani taro a Nairobin Kenya, Raila Odinga ya bayyana cewa, ya kamata cike gibin kudin aiwatar da ayyukan more rayuwa ya zama muhimmi ga samar da ci gaban nahiyar Afrika.

Ya ce, nahiyar Afrika na ci gaba da fama da karancin ababen more rayuwa, yanayin dake da matukar muhimmanci, la'akari da cewa, matsakaicin gibin kudin aiwatar da ayyukan ya kai dala biliyan 170.

Ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da ababen more rayuwa ke takawa ga samar da ci gaba da raya harkokin cinikayya, inda kuma ya koka da rashin ci gaban da ake samu wajen cike gibin.

Ya yi kira da a kammala babbar hanyar mota da ta ratsa kasashen yamma da Saharar Afirka da layin dogo na jiragen kasa masu matukar sauri da gadar da ta ratsa Kinshasa da Brazzaville da babbar hanyar da ta hada Lagos da Abidjan da Dakar, yana mai bayyana su a matsayin masu muhimmanci ga hada biranen nahiyar da samar da ayyukan yi ga kasashe mambobin AU.

Raila Odinga ya yi kira da hadin kan Afrika, yana mai cewa, ta hanyar hadin kai, nahiyar za ta kara karfin tasirinta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China