in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta gabatarwa AU kunshin amincewa da yarjejeniyar AFCFTA
2019-04-12 10:13:08 cri

A jiya ne, gwamnatin kasar Habasha ta gabatarwa hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka (AU) matakan amincewa da yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta Afirka (AFCFTA).

Ya zuwa yanzu dai kasashen Afirka 22 ne suka amince da yarjejeniyar, yayin da kasashe mambobin AU 19 suka gabatarwa kasashe mambobin kungiyar 55 matakansu na amincewa da yarjejeniyar.

Wata sanarwa da kungiyar ta AU ta fitar a jiya Alhamis na cewa, ana sa ran kasashen Saliyo da Zimbabwe da Gambia, za su gabatar da shaidar amincewa da wannan yarjejeniya, bayan da majalisun dokokin kasashensu suka amince da ita.

Kungiyar AU ta sanar da cewa, yarjejeniyar AFCFTA za ta fara aiki ne, wata guda bayan da kasashe 22 suka amince da ita, adadi mafi kankanta da ake bukata kafin ta fara aiki.

Shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat, ya bayyana cikin wata sanarwa bayan matakin gwamnatin kasar Habasha na goyon bayan yarjejeniyar cewa, amincewa da yarjejeniyar da mahukuntan kasar suka yi, ya nuna kudirin gwamnatin kasar da ma jagorancin firaminista Abiy Ahmed na ciyar da ajandar dunkulewar nahiyar gaba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China