in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na shirin kafa asusun samar da karin ababan more rayuwa a Afirka
2019-04-12 11:06:37 cri

Babban wakilin kungiyar tarayyar Afirka (AU) mai kula da raya kayayyakin more rayuwa a Afirka Raila Odinga, ya bayyana cewa, ana nan ana shirye-shiryen kafa wata gidauniya, da za ta kara fadada hanyoyin sunfurin da ake da su a sassan nahiyar.

Raila odinga ya bayyana hakan ne, yayin bikin rufe taron masana kan yadda za a gina titin jirgin kasa mai saurin tafiya na Afirka, wanda ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya. Yana mai cewa, kayayyakin more rayuwar nahiyar sun zama tsohon yayi, kuma kimanin kaso 60 cikin 100 na al'ummar nahiyar, ba su da hanyoyi da titunan dogo na zamani.

Ya ce, ofishinsa zai kira wani taro a mako mai zuwa, don duba yadda za a yi amfani da kudaden ceto dake ajiye a kasashen Afirka wajen inganta kayayyakin more rayuwa a nahiyar.

Jami'in ya kuma shaidawa masana da suka halartar taron dandalin na yini biyu, yadda za a hade nahiyar da layin dogo mai saurin tafiya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China