in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da tsarin inganta kulawa da tsoffi
2019-04-17 10:04:58 cri

Babban ofishin majalisar gudanawar kasar Sin, ya fitar da wani tsari na inganta kula da tsoffi da kuma biyan mabanbantan bukatunsu

Tsarin ya jadadda bukatar kafa wani tsari na sa ido kan hidimomin kula da tsoffi da zurfafa sauya fasalin cibiyoyin kula da tsoffi da jama'a ke bayar da kudin kula da su da kuma inganta kudin da gwamnati ke warewa ga kula da tsoffi.

Tsarin na bukatar fadada hanyoyin zuba kudi don cimma fadada samar da aikin yi da sana'o'i. Har ila yau, za a kafa wani tsari domin karfafa basirar masu bada kulawa da zummar samar musu da karin ilimi da damarmakin horo.

Baya ga haka, tsarin ya kuma bukaci kare bukatu da hakkokin tsoffi da kuma magance yadda ake tara kudi domin kula da su ba bisa ka'ida ba. ya kara da cewa, ya kamata a yi kokarin samar da ingantacciyar kulawa ga tsoffi da inganta cibiyoyin kula da su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China