in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu ingantuwar tsarin kula da tsoffi a kasar Sin
2019-04-01 21:22:52 cri
Rahotanni daga kasar Sin na cewa, an samu ingantuwar tsarin kula da tsofaffi a kasar, inda ya zuwa karshen shekarar 2018 da ta gabata, hukumomi da cibiyoyin kula da lafiyar tsofaffi 163,800 suka samarwa tsofaffi gadaje miliyan 7.46.

Yayin da ake kara samun tsoffi a cikin al'ummar kasar Sin, hukumomin kula da harkokin jama'a ke kaddamar da matakai, domin inganta hukumomin dake samar da hidima ga tsofaffi, ciki har da kara bude kasuwar kula da manya nan da shekarar 2020.

Ya zuwa karshe shekarar 2018, kaso 48 cikin 100 na hukumomin kula da tsofaffi dake kasar, masu zaman kansu ne.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China