Gao Xiaobing, mataimakin minista mai kula da al'amuran walwalar jama'ar kasar, ya tabbatar da hakan a taron 'yan jaridu a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, ya ce hukumomin gudanarwar kasar sun yi binciken dukkan gidajen kula da tsoffi wadanda aka yiwa rajista da wadanda ma ba'a yiwa rajistar ba.
Gao ya ce, a sakamakon hakan, matsalolin da gidajen kula da tsoffin kasar ke fuskanta ya yi matukar raguwa a rubu'in watanni ukun shekarar 2017 da ta gabata.
Kasar Sin tana samun karuwar adadin tsoffi. A halin yanzu, yawan mutanen da shekarunsu ya zarta 60 ya kai miliyan 241. Kana gidajen kula da tsoffi mallakar gwamnati ya yi karanci.
Mataimakin ministan ya ce, gwamnatin kasar za ta bullo da wani shiri na musamman wanda zai kara bunkasa ingancin gidajen kula da tsoffi, da kuma samar da wani tsari na kafa cibiyoyin kula da tsoffi karkashin tallafin al'umma ga tsoffin da suka fi sha'awar zama a cikin gidajensu, wanda ya dace da tsarin ka'idojin kula da tsoffi na kasar.(Ahmad Fagam)