in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mayakan IS a Somaliya
2019-04-16 11:09:07 cri

Ma'aikatar watsa labarai ta kasar Somaliya, ta ce jami'an tsaron kasar da hadin gwiwar rundunar sojin Amurka mai tallafawa kasar, sun hallaka wasu manyan kusoshin kungiyar IS a jihar Puntland dake kasar.

Rahotanni na cewa, an hallaka kwamandan kungiyar mai suna Abdihakim Mohamed Ibrahim, da wani mayakin guda daya, yayin wani samame da aka kaddamar kan maboyar su dake unguwar Hiriro, a garin Iskushuban dake karkashin lardin Bari.

Mayakan dai na cikin gungun kungiyar dake alakanta kan ta da IS, wadda ta balle daga kungiyar al-Shabab a watan Oktoban shekarar 2015, daga bisani kuma ta kame yankin Qandala, wani wuri mai muhimmanci a garin Bari na jihar Puntland dake arewacin kasar ta Somaliya.

Kawo yanzu dai Amurka ba ta ce komai ba game da aukuwar harin, wanda ke zuwa yayin da Amurkar ke kara kaimi, wajen tallafawa Somaliya a yakin ta da 'yan tada kayar baya cikin 'yan shekarun baya bayan nan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China