in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar AU ta kammala wata ziyara a Somaliya
2018-11-29 13:14:46 cri

A jiya ne wata tawaga daga sashen wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka (PSD) ta kammala wata ziyaryar kwanaki uku da ta kai a kasar Somaliya, inda take kira da a aiwatar da shirin mika mulkin kasar kamar yadda matakan tsaron kasar suka tanada.

Tawagar mai mambobi 27 karkashin jagorancin jakadan kasar Djibouti a kasar Habasha Mohamed Idriss ta kuma yi alkawarin nazartar yanayin da ake ciki a kasar dake yankin kahon Afirka.

Idriss ya ce, suna fatan taron da manyan jagororin soja daga kasashe 6 dake ba da gudummawa sojoji (TCCs) da zai gudana gobe Jumma'a zai bullo da sabbin dabarun da za su taimakawa tawagar AU dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar ta Somaliya(AMISON).

Jakadan ya ce, hukumar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta AU, za ta bukaci shawarwari daga taron kwamitin dake tsare ayyukan soja (MOCC), wanda zai hallara jagororin sojojin kasashen 6 da manyan abokan hulda da ma jagororin tawagar AMISON.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China