in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Somaliya sun bukaci hadin kai a lokacin tunawa da wadanda suka mutu a harin Oktoba
2018-10-15 09:36:52 cri

A jiya Lahadi kasashen duniya suka bi sahun al'ummar kasar Somaliya domin nuna juyayin mutuwar mutane 587 da jikkata 316 a harin ta'addanci da aka kaddamar a ranar 14 ga watan Oktoban 2017 a Mogadishu.

Yan kasar Somaliya da suka hada da 'yan majalisar dokokin kasar da jami'an gwamnati sun yi amfani da wannan lokaci wajen yin kiraye kiraye na hada kai, da tabbatar da zaman lafiya da cimma daidaito wanda zai kawo dawwamamman zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Dubban 'yan kasar Somaliya ne suka yi gangami a yankin Zoope Junction, wajen da aka kaddamar da mummunan harin bom din domin tunawa da 'yan uwansu da abokan arzikin da suka mutu, inda aka tsaurara matakan tsaro a wajen da kewayensa a birnin Mogadishu.

Daruruwan mutane sun ziyarci wajen da aka yiwa suna K-5 junction, inda aka hallaka daruruwan mutanen a ranar 14 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Da yake jawabi a lokacin gangamin, firaiministan kasar Hassan Khaire ya bayyana harin ta'addancin na watan Oktoban shekarar 2017 a matsayin harin ta'addanci mafi muni a tarihin kasar.

Khaire ya ce, daruruwan mutanen da suka tsira a sanadiyyar harin har yanzu suna ci gaban da jiyya, inda wasu suka samu raunuka a gangar jikinsu, wasu kuma ta fuskar tunaninsu, don haka ya gargadi mutanen Somaliya da su guji barin 'yayansu su shiga kungiyoyin ta'addanci. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China