in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci sabon kwamandan rundunar wanzar da zaman lafiya murkushe mayakan al-Shabab
2019-02-01 11:01:35 cri

Babban jakadan kungiyar tarayyar Afrika AU ya bukaci sabon kwamandan rundunar wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU a Somalia, Tigabu Yilma Wondimhunegn, dan asalin kasar Habasha da ya jajurce wajen fatattakan mayakan al-Shabab a kasar ta gabashin Afrika.

Francisco Madeira, wakilin musamman na kungiyar tarayyar Afrika a Somalia, ya ce har yanzu akwai ayyuka masu yawa wadanda ya kamata a kammala gabanin tawagar ta kawo karshen wa'adin aikinta a kasar.

Wondimhunegn, ya karbi aiki ne daga hannun kwamanda Jim Beesigye Owoyesigire, wanda ya kammala wa'adin aikinsa da ya fara tun a watan Janairun shekarar 2018.

Dakarun kiyaye zaman lafiyar na AU suna ci gaba da farautar 'yan tada kayar baya wadanda ke kaddamar da hare hare da nufin kifar da gwamnatin kasar Somalia.

Wondimhunegn, yana da kwarewar aiki na shekaru 34 a fagen aikin soji kuma ya taba yin aiki a matsayin babban hafsan tsaro na rundunar sojojin kasar Habasha a matakai daban daban.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China