in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alibaba zai kaddamar da darussan kasuwancin zamani ga daliban Rwanda
2019-04-16 09:50:03 cri

Babban kamfanin cinikayya ta yanar gizo na kasar Sin wato Alibaba, ya shirya kaddamar da wasu darussan musamman domin dalibai 'yan kasar Rwanda, domin samar musu da horo a fannin amfani da yanar gizo a harkokin cinikayya.

Fannin samar da horo na kamfanin Alibaba, ya tanaji tsarin samar da horo na kasa da kasa a wannan fanni, wanda a bana, karkashin sa za a baiwa dalibai 'yan Rwanda su 30 damar samun horo na shekaru 4 a birnin Hangzhou, helkwatar kamfanin na Alibaba. Daliban za su samu horo a fannonin sarrafa yanar gizo, da kasuwancin kasa da kasa, da kuma cinikayya tsakanin nahiyoyi.

Tsarin dai wani muhimmin bangare ne na yarjejeniyar da aka sanyawa hannu a bara, tsakanin kasar Rwanda da kamfanin na Alibaba, wadda ke da nufin samar da dama ta hade sassan duniya wuri guda a fannin cinikayyar yanar gizo.

Kasar Rwanda ce kasar Afirka ta farko da ta kaddamar da wannan tsari, na amfani da yanar gizo wajen bunkasa hada hadar cinikayya.

Babban daraktan hukumar ilimi mai zurfi a kasar Emmanuel Muvunyi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, burin kasar Rwanda shi ne samar wa matasa damar samun horo, a fannin fasahar sadarwa, da za su bukata domin inganta rayuwar su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China