Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya bukaci a gudanar da bincike kan matakan kariya a rukunonin kantuna, bayan mummunar gobarar da ta tashi a birnin Kemerovo na yankin Siberia dake kasar.
Sanarwar da fadar Kremlin ta fitar ta ce, Putin ya ba da umarnin ne yayin wani taro kan tattalin arziki da aka yi a jiya.
Da tsakar ranar Lahadi ne wata mummunar gobara ta tashi a rukunin kantuna na Winter Cherry dake birnin Kemerovo na kasar, inda ta yi sanadin mutuwar mutane 64.
Shugaba Putin ya umarci gwamnatin tarayyar kasar da hukumomin yankin, sun ba da dukkan taimakon da ake bukata ga iyalan wadanda suka mutu ko suka jikkata yayin gobarar.
A wani taro na daban da shugaban kwamitin bincike na kasar da ministan lafiya a jiyan, shugaban kasar ya jadadda cewa, tilas ne a gudanar da bincike kan tashin gobarar bisa gaskiya da adalci. (Fa'iza Mustapha)