in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
SADC ta kira a samar da tallafi ga mutanen da guguwar Idai ta shafa
2019-04-12 13:39:27 cri

Shugaban kungiyar raya shiyyar kudancin Afrika (SADC) kana shugaban kasar Namibia Hage Geingob a ranar Alhamis ya kira a samar da tallafi ga mutanen da mahaukaciyar guguwar iskar Idai ta shafa a shiyyar.

Da yake jawabi a Windhoek, babban birnin kasar Namibia, Geingob ya ce, mahaukaciyar guguwar iskar ta yi sanadiyyar haifar da mummunar barna ga tattalin arziki da kayayyakin more rayuwa, lamarin da ya sa ake bukatar daukin gaggawa, da na matsakaicin lokaci da kuma dauki na dogon zango."

Sannan ya bukaci a gudanar da hadin gwiwa wajen tunkarar matsalolin da yankin ya fada.

Kimanin gonaki masu girma hekta 800,000 na amfanin gona bala'in ya lalata, baya ga wata babbar matsalar fari wadda ta haddasa kamfar abinci a kasashen da bala'in ya shafa. Mahaukaciyar guguwar ta kuma lalata hanyoyin mota da gidajen kwanan jama'a, lamarin da ya jefa al'ummomin yankin cikin yanayin bukatar kayayyakin agajin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China