in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar ba da agajin Sin ta kammala aiki a Mozambique
2019-04-04 19:29:36 cri

A daren jiya ne, agogon kasar Mozambique, tawagar masu aikin sa kai dake ba da agaji ta kasar Sin ta bar kasar, bayan da ta kammala aikin ba agaji cikin nasara ga wadanda mahaukaciyar guguwar nan ta Idai ta yiwa barna, yayin aikinsu a kasar, masu aikin sa kai na kasar Sin sun samar da ceton jinya ga masu bukata, tare kuma da tantance hadarin masifar, domin kubutar da masu fama da masifa daga mawuyacin yanayi. Adadin marasa lafiya da suka samu taimakon masu aikin ba da agajin kasar ta Sin ya kai 3337, fadin wuraren da suka tsabtace ya kai muraba'in mita dubu 330.8, kana sun samar da abinci da magunguna da ruwa ga masu fama da iftila'i a kasar sama da dubu daya cikin gaggawa.

Babban jagoran ofishin kula da harkokin jin kai na MDD dake Mozambique Sebastian Rhodes Atampa ya bayyana cewa, tawagar ba da agajin kasar Sin da kungiyoyin MDD suna gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu lami lafiya, kwazon aikin tawagar kasar Sin ya burge shi matuka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China