in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya yi kira da a kara taimakawa wadanda mahaukaciyar guguwar Idai ta shafa
2019-04-11 10:07:32 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya yi kira ga 'yan kasuwa da ragowar masu ruwa da tsaki, da su taimaka wajen sake gina kayayyakin more rayuwar jama'a da mahaukaciyar guguwar nan ta Idai ta lalata a sassan kasar cikin watan Maris din wannan shekara.

Shugaban ya yi wannan kira ne, yayin wata ganawa da 'yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a fadar gwamnatin kasar. Shugaban ya kuma wallafa sakon godiya a shafinsa na Tweeter dangane da karanci da kauna gami da aniyar da wasu kamfanoni suka nuna ta daukar nauyin gyara wasu makarantu da ababan more rayuwar jama'a da mahaukaciyar guguwar ta Idai ta daidaita, da gudummawar kayayyaki da aka ba, da ma yadda ake ciyar da wasu daliban makarantu abinci sau uku a rana.

Taron na zuwa ne, kwana guda bayan da gwamnatin kasar ta ce, tana bukatar a kalla dala miliyan 612 don sayen abinci da gina matsuguni da sauran muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, biyo bayan barnar mahaukaciyar guguwar ta Idai, wadda ta halaka mutane da yawansu ta kai 344, adadin da ake fargabar na iya karuwa, yayin da ake ci gaba da gano gawawwaki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China