in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da ministan tsaron Sudan a matsayin shugaban majalisar rikon kwaryar kasar
2019-04-12 11:09:52 cri

Ministan tsaron kasar Sudan Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf a jiya Alhamis aka rantsar da shi a matsayin shugaban majalisar gudanarwar rikon kwarya na kasar, gidan talabijin din Sudan TV ne ya ba da rahoton.

Tun da farko a ranar Alhamis, Ibn Auf ya ba da sanarwar hambarar da gwamnatin shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir.

Kana ya kuma ba da umarnin kafa dokar ta baci na tsawon watanni 3 a kasar da kuma dokar takaita zirga zirga ta tsawon wata guda.

Ministan tsaron ya ce, majalisar sojojin kasar ce za ta ci gaba da jan ragamar shugabancin kasar har zuwa lokacin da za'a kafa sabuwar gwamnati cikin wa'adin shekaru biyu.

Ya kuma sanar da yin watsi da kundin tsarin mulkin kasar Sudan na wucin gadi, tare da rufe filin jirgin saman kasar na tsawon sa'o'i 24 da rufe dukkan kan iyakokin kasar Sudan har sai abin da hali ya yi.

Tun a ranar 19 ga watan Disamban bara, Sudan take ci gaba da fuskantar zazzafar zanga zangar nuna adawa kan tabarbarewar yanayin tattalin arziki da tsadar kayan masarufi da kasar ke fama da da su.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China