in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojojin Sudan na shirin fitar da wata muhimmiyar sanarwa
2019-04-11 14:38:03 cri

Rahotanni daga kasar Sudan na cewa, rundunar sojan kasar, za ta fitar da wata muhimmiyar sanarwa dangane da halin da kasar ke ciki.

Shaidun gani da ido na cewa, sojoji sun kara tsaurara matakan tsaro a harabar ginin rediyo da talabijin na kasar. Yanzu haka dai, gidan talabijin na kasar, ya katse watsa shirye-shiryensa, inda ya fara watsa taken kasar.

A ranakun Asabar da Lahadi ne dai, dandazon jama'a a Khartomun, babban birnin kasar suka bazama tituna suna bore, inda suka karkare da yin zaman dirshan a gaban hedkwatar rundunar sojojin kasar.

Tun a ranar 19 ga watan Disamban shekarar da ta gabata ce, 'yan kasar ke bore sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da kuma hauhawar farashin kayayyakin masarufi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China