in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Chadi yana ziyara a Sudan
2019-04-04 20:51:36 cri

A yau ne shugaba Idriss Deby na kasar Chadi ya isa Khartoum, babban birnin kasar Sudan, don fara wata ziyarar aiki ta yini guda.

Shugaba Omar al-Bashir na Sudan da jami'an kasar da wakilan ofisoshin jakadancin kasashe daban-daban da dama dake Sudan ne suka tarbe shi a filin saukar jiragen saman kasar.

Ana sa ran shugabannin kasashen biyu, za su gana a fadar shugaban kasa, inda za su tattauna batutuwan shiyya da wadanda ke shafar su. Za kuma su tattauna kan bunkasa alaka tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama.

Daga bisani shugabannin biyu, za su yiwa manema labarai bayanai game da sakamakon ziyarar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China