in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi kira ga al'ummar Sudan da su kwantar da hankali
2019-04-12 09:03:45 cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya sake yin kira ga al'ummar kasar Sudan, da su kwantar da hankali tare da kai zucuiya nesa, bayan da sojoji suka hambarar da Omar al-Bashir da ya dade yana jan ragamar mulkin kasar.

Guterres wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da mai magana da yawunsa Stephane Dujarric ya fitar, ya ce za a kare muradun demokiradiyar al'ummar Sudan ta hanyar shirin mika mulki da ya dace.

Ya kuma nanata cewa, a shirye MDD ta ke, ta goyi bayan al'ummar kasar Sudan yayin da suke kokarin neman sabuwar hanyar ci gaba.

Sai dai da aka tambaye shi ko MDD ta tuntubi sabuwar gwamnatin dake Khartoum, sai Dujarric ya ce, har yanzu babu wani karin bayani daga ofishinsu, amma dai yana da imanin cewa, nan ba da dadewa ba, majalisar za ta tuntubi sabbin mahukuntan kasar ta Sudan.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China