in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce kura ta lafa a Juba, sai dai har yarzu ana zaman dar dar
2016-07-19 11:05:01 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Sudan ta kudu (UNMISS) ta ba da rahoton cewar, kura da lafa a Juba babban birnin kasar, sai dai har yanzu ana zaman zulumi, sakamakon karin harbe harbe da ake samu tun a karshen wannan mako a wasu wuraren, ciki har da ofishin na UNIMISS.

Mataimakin mai magana da yawun MDD Farhan Haq, ya shedawa 'yan jaridu cewa, ana ci gaba da binciken makamai a yankuna dake daura da harabar MDD da nufin samar da kariya ga fararen hula.

A sakamakon binciken, an bankado wasu tarin makamai da suka hada da abubuwan fashewa, da kananan bingigogi, da alburusai, da kayayyakin sojoji.

Sanarwar ta kara da cewa, kimanin ma'aikatan UNMISS 140 ne aka kwashe daga Juba, sai dai har yanzu tagawar wanzar da zaman lafiyar tana ci gaba da gudanar da aikinta.

Ofishin sashen ba da jin kai na MDD (OCHA) ya rawaito cewa, an samu karuwar sansanin 'yan gudun hijira a Juba, wadanda ke zaune a harabar ofisoshin MDD dake birnin.

Mutanen da rikicin na baya bayan nan ya tilastawa ficewa daga gidajensu ya tasamma dubu 15, kana sama da mutane dubu 10 da 830 na zaune a yankunan ofishin na UNMISS, sannan sama da mutane 4,100 na wajen ofishin. Kungiyoyin ba da agaji na ci gaba da kai daukin gaggawa ga yankunan da matsalar ta yi kamari.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China