in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin: Ya kamata a martaba ikon shari'ar kasar Sudan
2018-12-15 19:51:55 cri

A jiya Juma'a ne zaunannen mataimakin wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao, ya bayyana cewa kasar Sin tana fatan kwamitin sulhun MDD, da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, da su martaba ikon shari'ar kasar Sudan, haka kuma su mai da hankali kan bukatun da gwamnatin kasar Sudan ta gabatar wa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa game da batutuwan dake shafar harkokin kasar ta Sudan, kana su amince da ra'ayoyin kungiyar tarayyar Afirka, da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa.

Jami'in ya kara da cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, yanayin tsaron da yankin Darfur na kasar Sudan ke ciki ya samu kyautatuwa sannu a hankali, a don haka kasar Sin ta yaba da kokarin da gwamnatin kasar Sudan take domin kiyaye zaman lafiya, kuma tana ganin cewa, gwamnatin Sudan tana da karfin kiyaye kwanciyar hankali, bisa dogaro da kanta a yankin. Ban da haka kuma, kasar Sin tana fatan kasashen duniya za su amince da ikon yanke shawara kan batun dake shafar yankin Darfur na gwamnatin Sudan, tare kuma da samar da taimako gare ta, ta yadda za a cimma burin tabbatar da kwanciyar hankali, da dauwamammen ci gaba a kasar ta Sudan.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China