in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya bukaci kananan kabilu su kara gina kyakkyawar makomar rayuwar al'umma
2019-04-11 15:14:33 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci al'ummun kananan kabilun kasar Sin dake zaune a yankunan kudu maso yammacin kasar da su gina ingantattun gidaje, su gudanar da tsaron kan iyakoki, kuma su gina ingantacciyar rayuwar nan gaba.

Xi ya yi wannan kira ne a ranar Laraba a lokacin da yake ba da amsa ga wasikar da 'yan karamar kabilar Dulong dake garin Dulongjiang na gundumar Gongshan na lardin Yunnan.

Cikin wasikar tasu, 'yan kabilar Dulong, sun sanar da shugaba Xi cewa, sun yi nasarar tsame dukkan al'ummarsu daga kangin fatara a shekarar 2018 kuma al'ummar kauyukansu suna jin dadin zaman rayuwarsu bisa yadda rayuwarsu ta kyautata.

Xi ya ce, yana matukar farin ciki da jin wannan labarin mai dadin ji, kuma ya taya al'ummar murna.

"Tabbatar da ganin dukkan al'ummun kabilu daban daban suna rayuwa cikin walwala da samun rayuwar mai kyau shi ne babban burina, kuma shi ne manufarmu ta bai daya," in ji shugaba Xi a sakon amsar da ya rubuta musu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China